Amurka

COVID-19: Yawan mutanen da suka rasa ayyukansu a Amurka ya haura miliyan 40

Wasu Amurkawa yayin layin neman hakkokin barin aiki a wani banki dake jihar Texas. 20/3/2020.
Wasu Amurkawa yayin layin neman hakkokin barin aiki a wani banki dake jihar Texas. 20/3/2020. REUTERS/Veronica G. Cardenas Food Bank

Bayaga halaka dubban rayukan da take yi a Amurka, annobar coronavirus na cigaba da yin tasiri wajen janyowa tattalin arzikin kasar koma baya ta fuskoki da dama ciki harda tafka hasarar miliyoyin guraben ayyukan yi.

Talla

Rahoton baya bayan nan da ma’aikatar kwadagon Amurkan ta fitar dai ya ce adadin mutanen da suka rasa guraben ayyukansu ya karu daga miliyan 36 zuwa sama da miliyan 40, sakamakon yadda tattalin arzikin kamfanoni ke durkushewa duk da sassauta dokar killace mutanen da gwamnati ta dauka don baiwa mutane damar komawa bakin aiki, da kuma farfado da tattalin arzikin kasar daga dogon suman da yayi.

Rabon da a ga irin wannan matsalar ta rashin aikin yi a Amurka, tun bayan matsanancin matsin tattalin arziki a farkon karni na 20.

Hasarar miliyoyin guraben ayyukanyin a Amurka dai na zuwa ne a daidai lokacin da sabbin alkalumma ke nuna cewa tattalin arzikin kasar ya durkushe da kashi 5 a watanni 4 na farkon wannan shekara ta 2020, saboda tasirin annobar coronavirus.

A yayinda ma'aikatar kwadagon Amurka ta fitar da rahoton dake nuna wasu Sabbin ma'aikata miliyan 2 da dubu 120 na ikirarin rashin samun tallafin albashi a karshen makon jiya, adadin na cigaba da karuwa fiye da kima.

Adadin masu neman tallafin albashin ya zarce na shekaru 12 da suka gabata, lokacin da kasar ta fada a matsalar tattalin arziki, sai dai adadin bai kai na mutane miliyan 2 da dubu 440 da aka samu a makon da ya gabata ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.