Amurka-WHO

Trump ya yanke alaka da Hukumar lafiya ta Duniya

Shugaban Amurka Donald Trump, yayin shelar yanke alaka da da hukumar Lafiya ta Duniya WHO.
Shugaban Amurka Donald Trump, yayin shelar yanke alaka da da hukumar Lafiya ta Duniya WHO. REUTERS/Jonathan Ernst

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana matakin yanke duk wata alaka da hukumar lafiya ta duniya WHO, abinda ke nufin daukar matakin dindindin na daina bata tallafin sama dala miliyan 400 duk shekara domin gudanar da ayyukanta.

Talla

Tsattsauran matakin da Trump ya bayyana a fadar White House a wannan Juma'a, yayin gabatar da jawabi kan makomar alakar Amurka da China na zuwa ne kwanaki, bayan da shugaba Trump ya zargi hukumar lafiyar ta duniya, da yin sakaci wajen daukar matakan dakile yaduwar annobar coronavirus daga China, da kuma zama ‘yar amshin shatar kasar ta China.

A gefe guda shugaba Trump ya kuma sanar da matakin haramtawa wasu manyan jami’an gwamnatin China shiga Amurka, biyo bayan tsamin da dangantakarsu tayi tun bayan zargin Chinan da kirkirar cutar coronavirus a dakin gwaje-gwajenta dake birnin Wuhan.

A cikin watan nan na Mayu shugaban Amurka Donald Trump, yace ba ya fatan sake yin magana da takwaransa na China Xi Jinping inda a fakaice ma yake cewa abu ne mai yiwuwa ya yanke duk wata alaka da kasar ta China, saboda takun sakar da kasashen ke yi da juna dangane da batun Coronavirus.

Trump ya bayyana haka ne, yayin zantawa da tashar talabijin ta ‘Fox Business’ inda yace a halin yanzu yana cikin fushi a game da halayen mahukuntan kasar ta China, kuma akwai hanyoyi da dama da zai iya daukar fansa akansu, ciki harda katse kowace irin hulda da kasar.

Trump ya share makwanni yana tuhumar China da kirkirar cutar coronavirus daga dakin gwaje-gwajenta a birnin Wuhan, duk da cewa kasar ta China na cigaba da musanta zargin, zalika binciken tawagar kwararrun hukumomin leken asirin Amurka ya nuna cewa, babu hannun dan adam wajen kirkirar cutar ko kuma sauya mata halitta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.