Mu Zagaya Duniya

Bitar muhimman abubuwan da suka faru a mako

Sauti 20:22
Taswirar duniya.
Taswirar duniya. Nations Online Project

Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan lokaci ya soma ne da waiwayar halin da duniya ke ciki dangane da annobar coronavirus ta fuskokin adadin rayukan da suka salwanta, da kuma yawan wadanda suka kamu da cutar. Shirin ya koma leka jihar Sokoto a Najeriya inda 'yan bindiga suka halaka akalla mutane 75, sai kuma Kaduna inda gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufa'i ya sha alwashin kawo karshen tsarin karatun almajiranci.