Kimiya

An yi nasarar harba kumbon farko mallakin kamfani mai zaman kansa zuwa wajen duniya

Kumbon 'yan sama jannati na Falcon-9 mallakin kamfanin SpaceX yayin tashi zuwa wajen duniya.
Kumbon 'yan sama jannati na Falcon-9 mallakin kamfanin SpaceX yayin tashi zuwa wajen duniya. Twitter/NASA

A karon farko cikin shekaru 9, an yi nasarar harba ‘yan sama jannati 2 daga Amurka cikin wani kumbo mallakin kamfanin SpaceX, zuwa wajen duniyar da muke domin bincike a sararin samaniya.

Talla

Kamfanin kera jiragen na ‘yan sama jannati mai zaman kansa dake Amurkan Space X da hadin giwar hukumar binciken sararin samaniya ta kasar NASA, ne suka jagoranci gagarumin shirin harba kumbon mai suna Falcon-9 a ranar asabar, 30 ga watan Yuni.

Falcon-9 ya tashi ne daga filin cibiyar binciken sararin samaniya ta Kennedy dauke da zakakuran jami’an hukumar NASA Robert Behnken da Douglas Hurley, daidai wajen da aka harba kumbon farko na Appollo 11 zuwa duniyar wata a shekarar 1969, karkashin jagorancin Neil Armstrong.

Ana sa ran kumbon na Falcon-9 zai shafe akalla sa’o’i 19 yana tafiya kafin kaiwa cibiyar bincike ta ISS dake da nisan kilomita 450 a sararin samaniyar dake wajen duniyar da muke.

Yanzu haka dai SpaceX ya kafa tarihin zama cibiya, ko kamfani mai zaman kansa da ya kera, tare da harba kumbonsa zuwa wajen duniya.

A shekarar 2002 mamallakin kamfanin Tesla da ya shahara wajen kera ababen hawa na zamani, Elon Musk ya kafa SpaceX da zummar cimma burin soma fita wajen duniya domin bincike a sararin samaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI