Kimiya

Kumbon SpaceX ya isa tashar binciken sararin samaniya dake wajen duniya

Jirgin 'yan sama jannati na 'Dragon Capsule' da kumbon Falcon-9 na kamfanin SpaceX, bayan isa tashar binciken kimiya ta ISS dake wajen duniya, dauke Douglas Hurley da Robert Behnken.
Jirgin 'yan sama jannati na 'Dragon Capsule' da kumbon Falcon-9 na kamfanin SpaceX, bayan isa tashar binciken kimiya ta ISS dake wajen duniya, dauke Douglas Hurley da Robert Behnken. © Nasa / Screenshot

Kumbon Falcon-9 mallakin kamfanin SpaceX mai zaman kansa ya isa tashar bincike ta kasa da kasa ISS dake sararin samaniyar wajen duniyar da muke.

Talla

A daren jiya asabar ne dai kumbon ya tashi daga Amurka dauke da jami’an hukumar biniciken sararin samaniya ta NASA guda biyu, Robert Behnken da Douglas Hurley, a daidai wajen da aka harba kumbon farko na Appollo 11 zuwa duniyar wata a shekarar 1969, karkashin jagorancin Neil Armstrong.

‘Yan sama jannatin dai sun shafe tafiyar akalla kilomita 450 zuwa wajen duniya kafin isa ga tashar binciken sararin samaniyar ta kasa da kasa da a takaice ake cewa ISS.

A shekarar 2002 mamallakin kamfanin Tesla da ya shahara wajen kera ababen hawa na zamani Elon Musk ya kafa SpaceX, kamfanin da a yanzu ya kafa tarihin zama na farko a tarihi da ya kera, tare da harba kumbonsa zuwa wajen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI