Amurka

Trump ya yi barazanar girke sojoji a tarzomar Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump na shan caccaka daga bangaren 'yan adawa da ke zargin cewa, yana rura wutar rikicin wariyar launi
Shugaban Amurka Donald Trump na shan caccaka daga bangaren 'yan adawa da ke zargin cewa, yana rura wutar rikicin wariyar launi MANDEL NGAN / AFP

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar girke dubban sojoji dauke da manyan makamai domin shawo kan tarzomar da ta karade sassan kasar sakamakon kisan gillar da wani dan sanda ya yi wa wani mutum bakar-fata.

Talla

A yayin gabatar da jawabinsa a dausayin Rose Garden da ke fadar White House a ranar Litinin, shugaba Trump ya ce, tilas ne magadan-gari da gwamnoni su dauki matakin kawo karshen wannan tarzoma, yana mai cewa, muddin suka gaza daukar matakan kare rayuka da dukiyoyin jama’arsu, to babu shakka zai girke sojojin Amurka da za su magance musu tashin hankalin.

A lokacin jawabin nasa, an yi ta wallafa wasu hotunan bidiyo a talabijin da ke nuna yadda jami'an tsaro ke amfani da borkonon-tsohuwa da harsashen roba wajen tarwatsa masu zanga-zanga a kusa da fadar White House.

Domin sanin halin da ake ciki yanzu haka a Amurka dangane da wannan zanga-zanga, kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa don sauraren cikakkiyar tattaunawar da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi da Alhaji Sulaiman Garba Krako Saminaka, mazaunin Amurka.

Tattaunawa tare da Alhaji Sulaiman Garba Krako Saminaka kan tarzomar Amurka

Tarzomar ta samo asali ne bayan wani hoton bidiyo ya nuna  jami'in 'yan sandan na  danne wuyar George Floyd mai shekaru 46 da guiwar kafarsa har tsawon minti tara a Minneapolis, abin da ya yi sanadin ajalinsa. Marigayin ya shaida wa dan sandan da abokan aikinsa cewa, ba ya iya numfashi.

Gwaji na biyu da aka yi wa gawar Floyd ya nuna cewa, kisan gilla aka yi masa ta hanyar amfani da karfi wajen hana shi numfashi.

Kazalika sakamakon gwajin ya nuna cewa, marigayin ya gamu da bugun zuciya a daidai lokacin da dan sandan ya tsare shi.

Tuni aka cafke dan sandan mai suna, Darek Chauvin, inda aka tuhume sa da aikata kisan kai a mataki na uku, yayin da aka kori wasu 'yan sanda uku daga bakin aikinsu bayan an zarge su da hannu a aika-aikar.

Shugaba Trump ya yi tur da kisan na Floyd, duk da cewa, ya bayyana masu tarzomar a matsayin ‘yan jagaliya.

Gwanayen caccaka sun soki  Trump wanda ke neman tazarce a zaben watan Nuwamba mai zuwa, inda suka zarge shi da rura wutar rikicin wariyar launi a  maimakon ya mayar da hankali wajen hada kan Amurkawa a cewarsu.

Ana sa ran ci gaba da gudanar da zanga-zangar duk da cewa, mahukunta sun kafa dokar takaita zirga-zirga a manyan biranen kasar da suka hada birnin New York, wanda hukumominsa suka sanya dokar kulle jama’a a gidajensu har zuwa karfe 5 na asubahin ranar Talata.

Sama da birane 75 suka gudanar da zanga-zangar adawa da kisan Floyd a Amurka, inda suka yi dandazo a cikin unguwannin da aka kaurace musu a kwanakin baya saboda annobar coronavirus.

Duk da cewa, har yanzu akwai fargabar yaduwar cutar coronavirus, amma masu boren sun yi ta tattaki kafada-da-kafada da juna.

Rahotanni sun ce, masu zanga-zangar sun kona motocin ‘yan sanda tare da cinna wa wasu gine-gine wuta, baya ga fasa shaguna da wawure abubuwan da ke cikinsu.

A bangare guda, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya bukaci masu tarzomar da su kwantar da hankula, sannan a gudanar da bincike dangane da zargin da ake yi wa ‘yan sanda cewa, da gangan suka kashe Floyd.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.