Kisan bakar-fata:Amurkawa sun zaburar da Faransawa
Dubban Faransawa sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da mutuwar wani matashi bakar-fata a hannun ‘yan sandan kasar a shekarar 2016, inda suke amfani da ire-iren kalaman da masu zanga-zanga a Amurka ke furtawa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Jami’an ‘Yan sandan Kwantar da Tarzoma sun cilla hayaki mai sa kwalla kan masu zanga-zangar a birnin Paris da zummar tarwatsa su saboda haramcin taruwar jama’ar da yawanta ya zarta 10.
Gabanin wannan sabuwar zanga-zangar, dimbin jama’a sun gudanar da tattakin lumana na tsawon sa’o’i biyu a daidai lokacin da wasu kasashen duniya suka fusata da kisan da aka yi wa George Floyd a Amurka.
Masu zanga-zangar na Faransa sun tuna tare da girmama marigayi Adama Traore, bakar-fatar da ya mutu a hannun jami’an ‘yan sandan kasar a shekarar 2016.
Kazalika an samu yamutsi a makamanciyar wannan zanga-zanga da aka gudanar a birnin Marseille da ke kudancin Faransa.
Zanga-zangar da aka gudanar a Amurka ta adawa da kisan da dan sanda ya yi wa Floyd, ita ce ta zaburar da Faransawa har suka gudanar da tasu zanga-zangar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu