Amurka

Masu zanga-zanga sun yi arangama da 'yan sandan Amurka

Dubban mutane sun fantsama kan titunan biranen Amurka domin ci gaba da gudanar da zanga-zangar adawa da kisan baka-fatar nan George Floyd, inda a wannan karo suka yi arangama da jami’an ‘yan sanda, yayin da wasu daga cikin masu boren suka fasa shaguna a birnin New York tare da wawure kayayyakin da ke cikinsu.

An raunata jami'an 'yan sanda biyar a yayin zanga-zangar adawa da kisan gillar da wani dan sanda farar-fata ya yi George Floyd bakar-fata
An raunata jami'an 'yan sanda biyar a yayin zanga-zangar adawa da kisan gillar da wani dan sanda farar-fata ya yi George Floyd bakar-fata Reuters
Talla

An gudanar gagarumar zanga-zangar a wurare da dama da suka hada da da Los Angeles da Philadelphia da Atlanta da Seattle, inda a birnin Washington DC, aka gudanar da zanga-zangar a kusa da dandalin da aka fatattaki masu bore a ranar Litinin domin share wa shugaba Donald Trump hanyar zuwa wata Majami’a mai cike da tarihi don daukar hoto.

Kodayake zanga-zangar ta kasance ta lumana a tsakar rana, amma jim kadan da fara shigowar dare, ta fara rikidewa zuwa tarzoma da fashe-fashe da kone-kone da kuma sace-sace, yayin da a daren Litinin, harsashin bindiga ya samu jami’an ‘yan sanda biyar a birane biyu.

A yammacin jiya Talata kuwa, masu zanga-zangar adawa da kisan Floyd, sun durkusa da guiwar kafa daya a harabar Majalisar Dokokin Amurka, inda suke fadin cewa, “ babu adalci, babu zaman lafiya”.

Masu boren dai sun ci gaba da zaman dirshen duk da dokar hana fita da mahukunta suka kafa, yayin da shugaba Trump ya lashi takobin daukar mataki kan abin da ya kira rashin bin doka da ‘yan daba ke yi, yana nufin dai masu zanga-zangar, sannan ya ce, akwai yiwuwar ya girke dubban sojojin da za su shawo kan lamarin.

Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da Kamfanin Dillancin Labaran Reuters ya gudanar, ta nuna cewa, kimanin kashi 64 na Amurkawa na tare da masu zanga-zangar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI