Brazil

'Yan Brazil dubu 30 sun mutu a sanadin coronavirus

Masu binne mutanen da coronavirus ta kashe a Brazil.
Masu binne mutanen da coronavirus ta kashe a Brazil. REUTERS/Amanda Perobelli

Adadin wadanda annobar Covid-10 ta kashe a Brazil a yanzu ya zarta mutane 30, abin da ya sa kasar ta zama daya daga cikin wadanda cutar ta fi yi wa ta’adi a duniya. 

Talla

Alkaluman da Ma’aikatar Lafiya ta fitar na nuni da cewa, an samu asarar rayukan mutane dubu 1 da 262 a cikin kwana daya a kasar, abin da ya sa Brazil ta zama kasa ta biyu da cutar ta fi saurin kisa a duniya baya ga Amurka.

Adadin mamatan ya karu ne a daidai lokacin da al'ummar kasar suka fara gudanar da harkokinsu na yau da kullum bayan an killace su a gidajensu na tsawon makwanni.

Gabanin wannan lokaci, Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da gaggauta sakin jama'a a Brazil.

A jumulce, mutane dubu 555 da 383 suka harbu da kwayar cutar coronavirus a Brazil.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI