Amurka

Kasashen duniya sun caccaki Amurka kan kashe Floyd

Hoton marigayi George Floyd bakar-fata da wani dan sanda farar-fata ya kashe a Amurka
Hoton marigayi George Floyd bakar-fata da wani dan sanda farar-fata ya kashe a Amurka Sergio Flores/Getty Images/AFP

Jagororin addini da ‘yan siyasa da shahararrun mawaka da kuma fitattun mutane a fannonin wasanni, sun bi sahun dubban mutanen da ke zanga-zanga a ciki da wajen Amurka wajen yin tur da kisan George Floyd a birnin Minneapolis. 

Talla

Yayin tur da kisan Floyd daga fadar Vatican, shugaban Darikar Katolika na Duniya Fafaroma Francis, kokawa ya yi kan yadda har yanzu aka gaza kawar da matsalar wariyar launi, wadda ya ce daukar mataki kanta ya zama tilas ta hanyar tabbatar da adalci, yayin da shi kuma jagoran addini a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatollah Ali Khamne’i ya bayyana abin da ya faru a Amurka a matsayin akidar kasar ta asassa zalunci, kamar yadda ake gani a Afghanistan da Iraqi da Syria da sauran kasashe bayan kwatanta hakan a Vietnam a shekarun da suka gabata.

Shahararrun mawaka a duniya ma ba a bar su a baya ba, ciki har da Rihanna da  Drake da Kylie Jenner, wadanda suka yi hutun aiki na kwana guda da kuma yada sakwanni ta shafukansu na kafofin sadarwar zamani don nuna goyon bayansu ga zanga-zangar kyamar halayyar nuna wariyar launi da cin zarafin dan Adam.

A nasu bangaren Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Turai sun yi tur da yadda matsalar wariyar launi ke ci gaba a fannonin lafiya da Ilimi da kwadago a Amurka, tare da bayyana kaduwa kan yadda  aka halaka Floyd.

A bangaren wasanni kuwa, a baya-bayan nan dan wasan Ingila Jadon Sancho ya sanya riga mai dauke da rubutun “a yi wa George Floyd adalci, tuni kuma takwarorin Sancho na kwallon kafa a sassan duniya suka rika durkusawa kan gwiwa daya yayin atisaye don alhinin abin da ya faru a Amurka da kuma mara wa masu zanga-zanga baya, abin da ya sanya wasu jami’ai tunanin hukunta 'yan wasan saboda saba dokar kauce wa bayyana sakwannin siyasa, to sai dai shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta duniya FIFA, Gianni Infantino ya ce kamata ya yi a jinjina wa yan wasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI