Amurka

Ministan tsaro ya kalubalanci Trump kan masu bore

Masu zanga-zangar neman yi wa marigayi Floyd adalci
Masu zanga-zangar neman yi wa marigayi Floyd adalci Mark Felix / AFP

Sakataren Tsaron Amurka Mark Esper ya kalubalanci matakin shugaban kasar Donald Trump na yin amfani da karfin soji kan masu zanga-zangar adawa da nuna wariya biyo bayan kisan da aka yi wa bakar-fatar nan George Floyd.

Talla

A yayin jawabin da ya gabatar ga taron manema labarai, Esper ya ce kamar yadda dokar kasar ta tanada, jami’an tsaro na National Guard ne za su ja da masu zanga-zangar sabanin dakarun sojoji da shugaban ke tunanin girkewa.

A cewar Esper, sam bai kamata a zartas da dokar da za ta bai wa soji damar dankwafe masu zanga-zanga ba, domin kuwa doka ta amince a yi amfani da sojojin ne  idan lamari ya fi karfin kulawar ilahirin jami’an tsaron da ke bayar da kariya a cikin kasa.

Kwana na 10 kenan da  dubun-dubatar masu zanga-zangar a biranen kasar kusan 40 ke gudanar da gangami don nuna bacin ransu tare da neman hakkin George Floyd da wani jami’in dan sandan Amurkan ya halaka har lahira a Minnesota.

Cikin kalamansa Esper ya ce, sam zanga-zangar kasar a yanzu ba ta kai matakin da za a ce ta fi karfin kulawar jami’an tsaro ba, domin kuwa ana gangamin ne cikin lumana, kodayake an samu fusatattun da suka barnatar da dukuyoyin al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.