Amurka

Floyd:'Bakaken fata za su samar da sauyi a Amurka'

Daruruwan masu zaman makoki sun halarci taron addu’ar tunawa da marigayi George Floyd, bakar-fatar nan da ‘yan sanda suka yi masa kisan gilla a birnin Minneapolis na Amurka, yayin da jagoran kare hakkin fararen hula, Al Sharpton ya lashi takobin ci gaba da gudanar da gagarumar zanga-zanga har sai an sauya daukacin tsarin shari’a a kasar.

Taron yi wa marigayi George Floyd addu'a a Minneapolis
Taron yi wa marigayi George Floyd addu'a a Minneapolis REUTERS/Lucas Jackson
Talla

Jim kadan da kammala taron addu’ar tunawa da Floyd, an ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana a birane da dama na Amurka, inda a birnin New York, dubban mutane suka yi tattaki akan babbar gadar Brooklyn, yayin da a Washington da Los Angeles aka dage dokar hana fita, amma an samu raguwar cinkoson jama’a.

A can birnin Minneapolis kuwa, lauyan iyalan Floyd, wato Benjamin Crump ya shaida wa mahalarta taron addu’ar cewa, zai nema wa marigayin hakkinsa a shari’ance.

Crump ya kara da cewa, ba cutar coronavirus ba ce ta yi sanadin ajalin Floyd mai shekaru 46, face wata annobar nuna wariyar launin fata.

A yayin girmama marigayin, mahalarta taron , sun mike tsaye tare da yin shiru na minti 8 da dakika 46, wato daidai tswon lokacin da dan sandan nan farar-fata ya shafe yana danne wuyan Floyd da guiwar kafarsa.

Kisan Floyd a ranar 25 ga watan Mayu, ya haddasa gagarumar zanga-zangar da ba a taba ganin irinta ba tun bayan kisan da aka yi wa Martin Luther King Jr a shekarar 1968.

Kazalila an gudanar da makamanciyar wannan zanga-zangar ta nuna adawa da kyamar bakake a kasashen duniya da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI