Lafiya

Turai za ta tallafa wa matalautan kasashe kan coronavirus

Masana kimiya na ci gaba da kokarin samar da riga-kafin cutar coronavirus
Masana kimiya na ci gaba da kokarin samar da riga-kafin cutar coronavirus REUTERS/Arnd Wiegmann

Kasashen yankin Turai sun cimma matsayar tashi tsaye kan aniyarsu ta tallafa wa kasashen da annobar coronavirus ta tagayyara tattalin arzikinsu. Kasashen Turan sun cimma matsayar ce yayin taron da kasashe sama da 50 suka halarta ta hoton bidiyon Intanet. 

Talla

Yayin jawabi a taron, Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya bukaci kafa sabon kawancen tunkarar matsalolin fannin lafiya tsakanin kasashen duniya tare da mayar da hankali kan kasashe matalauta.

Daga bisani, kasashen sama da 50 suka cimma matsayar raya katafariyar gidauniya ta binciken maganin cutar coronavirus da kuma gaggauta samar da allurar rigakafin annobar, gami da rarraba su zuwa kasashe masu tasowa.

Wannan sabon yunkuri ya zo ne a daidai lokacin da nahiyar Kudancin Amurka ta zama sabuwar cibiyar annobar coronavirus, inda cikin sa’o’i 24 da suka gabata cutar ta halaka mutane dubu 1 da 349 a Brazil, yayin da a Mexico ta halaka wasu rayukan sama da dubu 1. Wannan ce ta sanya Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres jaddada bukatar samar da maganin wannan annoba ga daukacin mutane cikin sauki.

Tun bayan bulla daga kasar China a watan Disambar shekarar bara, coronavirus ta halaka sama da mutane dubu 387 daga cikin sama da mutane miliyan 6 da rabi da suka kamu, annobar ta kuma tagayyara tattalin arzikin duniya, bayan tilasta killace mutane a gida tsawon watanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI