Amurka

Dubban mutane sun shirya gagarumar zanga-zanga a Amurka

An yi amfani da kafafen sada zumunta wajen gayyatar miliyoyin mutane da su shiga zanga-zangar adawa da kisan Floyd
An yi amfani da kafafen sada zumunta wajen gayyatar miliyoyin mutane da su shiga zanga-zangar adawa da kisan Floyd Angela Weiss / AFP

Ana sa ran dimbin masu zanga-zanga su yi dandazo a birnin Washington na Amurka a daidai lokacin da aka shiga rana ta 12 da fara gagarumin tattaki a sassan kasar, inda jama’a ke nuna bacin ransu da kisan gillar da jami’an ‘yan sanda suka yi wa bakar-fatar nan George Floyd.

Talla

Masu Rajin Kare Hakkin Bil’adama sun yi amfani da kafafen sada zumunta wajen kira ga miliyoyin mutane da su shiga zanga-zangar ta yau a babban birnin Amurka da New York da Miami da kuma Minneapolis.

Tuni jami’an ‘Yan sanda suka killace harabar fadar gwamnatin White House gabanin kaddamar da gagrumar zanga-zangar ta yau.

A watan jiya ne wani hoton bidiyo da aka wallafa a shafin sada zumunta ya nuna yadda wani dan sanda mai suna Darek Chauvin ya danne wuyan Floyd da guiwar kafarsa na kusan minti tara, lamarin da ya yi sanadin ajalinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.