Coronavirus

Coronavirus ta lakume rayuka fiye da dubu 400

Yadda ake jana'izar mutanen da coronavirus ta kashe a Brazil
Yadda ake jana'izar mutanen da coronavirus ta kashe a Brazil REUTERS/Amanda Perobelli

Sabuwar annobar coronavirus ta kashe mutane sama da dubu 400 a sassan duniya tun bayan bullarta a karshen shekarar bara a China kamar yadda sabbin alkaluman hukumomin lafiya na duniya suka nuna a yau Lahadi.

Talla

Kimanin mutane miliyan 6 da dubu 900 suka kamu da cutar a kasashen duniya 196 kamar yadda Jami’ar Johns Hopkins ta sanar, amma fiye da miliyan 3 sun warke daga annobar.

A Amurka kadai, an samu asarar rayukan mutane dubu 109 da 802, sai Birtaniya, inda aka samu mutuwar mutane dubu 40 da 465, yayin da a Brazil, cutar ta lakume rayuka dubu 35 da 930.

Cutar ta kashe mutane fiye da dubu 175 a nahiyar Turai kadai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI