Italiya

Italiya ta rabu da bala'in coronavirus-Fafaroma

Fafaroma Francis
Fafaroma Francis REUTERS/Remo Casilli

Shugaban Darikar Katolika ta Duniya Fafaroma Francis da ke jawabi ga mabiyansa a dandalin Saint Peters, ya ce, bala’in cutar coronavirus ya kawo karshe a Italiya.

Talla

A karon farko kenan da Fafaroman ke jawabi ga taron mabiya tun lokacin da aka kafa dokar ta baci a bangaren kiwon lafiya a kasar ta Italiya.

Kodayake Fafaroman ya gargadi jama’a da su yi taka-tsan-tsan tare da mutunta ka’idojin nesa nesa da juna, yana mai cewa, kar su yi gaggawar fara murnar cin galabar cutar.

Fadar Vatican dai ta ce, yanzu babu mutun ko guda daga cikin ma’aikatanta da ke dauka da cutar ta coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI