Jamus-amurka

Jamus ta kadu da shirin Trump na janye dakarunsa a kasar

Gwamnatin Jamus ta bayyana damuwarta game da rahotan da ke cewa, shugaba Donald Trump na shirin rage yawan dakarun Amurka da aka girke a Jamus.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. Reuters/路透社
Talla

Ministan Harkokin Wajen Jamus, Heiko Maas ya ce, kasashen biyu sun tsaya haikan domin su amfanar da juna koda kuwa alakarsu ta samu koma-baya a karkashin mulkin shugaba Trump.

Da dama daga cikin fitattun ‘yan siyasar Jamus sun caccaki matakin da suka bayyana a matsayin gagarumin cikas kan huldar kasashen biyu da kuma barazanar tsaro da hakan zai haifar.

A ‘yan shekarun nan dai, shugaba Trump na yawan sukar Jamus da ta kasance daya daga cikin mambobin kungiyar tsaro ta NATO, yana mai zargin ta da nokewa wajen kashe kudade kan harkar tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI