Isra'ila

Netanyahu ya ji takaicin kisan da aka yi wa Bafalasdine

Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu Gali Tibbon/Pool via REUTERS

Firaministan Isra’ila Benjamin Natanyahu ya ce, kisan da jami’an ‘yan sandan kasar suka yi wa wani Bafalasdine mai fama da larurar kwakwalwa, abin tausayi ne da kuma rashin adalci, yayin da ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan marigayin.

Talla

A ranar 30 ga watan Mayu ne, ‘Yan sandan Isra’ila suka harbe Iyak Hallak mai shekaru 32 har lahira a birnin Kudus, a daidai lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa makarantar nakasassu .

Jami’an tssaron su ce, sun zaci Hallak na dauke da makami ne, yayin da Netanyahu ya ce, yana dakon sakamakon binciken da aka kaddamar kan lamarin don daukar mataki na gaba.

Dubban masu alhinin mutuwarsa ne suka halarci jana’izar matashin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI