Amurka

Zanga-zangar kisan Floyd ta dauki sabon salo a Amurka

Wasu daga cikin masu zanga-zangar nuna bacin ransu da kisan gillar da aka yi wa George Floyd a Amurka
Wasu daga cikin masu zanga-zangar nuna bacin ransu da kisan gillar da aka yi wa George Floyd a Amurka REUTERS / Caitlin Ochs

Zanga-zangar nuna bacin rai kan kisan da ‘yan sanda suka yi bakar-fatar nan, Geroge Floyd ta dauki sabon salo, inda a karshen makon nan, masu boren da suka yi dandazo a biranen Amurka da suka hada da Washington da Texas ke neman hukumomi da su yi adalci dangane da matasalar wariyar launi.

Talla

Masu boren dai sun zaburar da jama’a a sassan duniya, inda aka gudanar da makamancin boren na Amurka a birnen Brisbane da Sydney da London da Paris da sauran manyan birane a kasshen Turai.

A birnin Washington dai, dubban masu zanga-zangar sun yi ta fadin cewa, “Bana iya numfashi” wato kalaman da marigayi Floyd ya yi ta furta wa dan sandan da ya danne wauyarsa da guiwar kafarsa.

Masu zanga-zangar sun yi daga allunan da ke cewa, rayuwar bakar-fata na da muhimmanci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.