Coronavirus

Mutane dubu 400 sun yi ban-kwana da duniya saboda coronavirus

Duniya ta girgiza a dalilin annobar coronavirus
Duniya ta girgiza a dalilin annobar coronavirus indiatimes

Sabuwar annobar coronavirus ta kashe mutane sama da dubu 400 a sassan duniya tun bayan bullarta a karshen shekarar bara a China kamar yadda sabbin alkaluman hukumomin lafiya na duniya suka nuna.

Talla

A jumulce, mutane dubu 400 da 581 aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus a sassan duniya, yayin da mutane miliyan 9 da dubu 949 da 890 suka harbu da ita a kasashe 196.

Sai dai mutane miliyan 3 da dubu 30 da 800 sun warke daga cutar a fadin duniya.

A Amurka kadai, an samu asarar rayukan mutane dubu 110 da 37, sai Birtaniya, inda aka samu mutuwar mutane dubu 40 da 542, yayin da a Brazil, cutar ta lakume rayuka dubu 35 da 930.

Sai kuma Italiya, inda aka samu asarar rayukan mutane dubu 33 da 899, yayin da a Faransa cutar ta halaka mutane dubu 29 da 155

Cutar ta kashe mutane fiye da dubu 175 a nahiyar Turai kadai, yayin da a nahiyar Afrika ta lakume mutane dubu 5 da 74.

China wadda ita ce makyankyasar wannan annoba, ta rasa jumullar mutane dubu 4 da 634.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI