Amurka

Trump ya janye dakarun da ya girke a Washington

Shugaban  Amurka Donald Trump ya umurci jami’an tsaron rundunar ‘National Guard’ da aka girke a Washington domin dakile masu zanga-zangar nuna bacin rai da kisan gillar da aka yi wa George Floyd da su janye daga birnin.

An girke rundunar tsaro ta National Guard ne domin tunkarar masu zanga-zangar adawa da kisan George Floyd
An girke rundunar tsaro ta National Guard ne domin tunkarar masu zanga-zangar adawa da kisan George Floyd Reuters
Talla

A sakon da ya saba aike wa ta kafar Twitter, shugaba Trump ya ce, ya umurci dakarun 'National Guard’ da su janye daga birnin Washington saboda abin da ya kira yadda al’amura suka daidaita.

Trump ya ce, ana iya sake maido da dakarun muddin bukatar haka ta sake tasowa.

Dubun-dubatar mutane sun sake gudanar da zanga-zangar lumana a Washington da kuma wasu biranen Amurka domin ci gaba da nuna bacin ransu da kisan gillar da 'yan sanda farar-fata suka yi wa Floyd, yayin da jami’an tsaro suka killace fadar shugaba Trump wadda aka kara tsayin shingenta.

A wata hira ta kafar Talabijin, tsohon Babban Hafsan Hafsoshin sojin Amurka, Colin Powell ya bayyana shugaba Trump a matsayin mai hadari ga dimokiradiyar Amurka wanda ya kauce wa dokokin kasa, inda yake cewa, a zabe mai zuwa zai kada wa Joe Biden na Jam’iyyar Democrat kuri’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI