Amurka

'Yan Majalisar Amurka sun sanya gwiwa kasa na minti 8 don jimamin kisan Floyd

Manyan 'yan Majalisar dokokin Amurka daga Jam’iyyar Democrat da suka hada da shugabar Majalisa Nancy Pelosi da shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa Chuck Schumer sun sanya gwiwar su a kasa har na tsawon mintuna 8 da dakikoki 46 domin karrama bakar fata George Floyd da wani dan sanda farar fata ya kashe a Birnin Minneapolis na jihar Minnesota a kasar.

Shugabar Majalisar Wakilan Amurka da wasu mambobin Majalisar 'yan Jam'iyyar Democrat yayin jimamin kisan George Floyd da 'yansanda Minnesota suka yi.
Shugabar Majalisar Wakilan Amurka da wasu mambobin Majalisar 'yan Jam'iyyar Democrat yayin jimamin kisan George Floyd da 'yansanda Minnesota suka yi. AP Photo
Talla

Yayin bayyana bacin ran su da kisan gillar da aka yiwa Floyd, shugabar Majalisar Pelosi ta ce Majalisar wakilai za ta gabatar da wata sabuwar doka wadda zata rage karfin Yan Sandan da kuma hukunta wadanda suka aikata irin wannan laifin.

Cikin jawabin Pelosi ta ce "cin zarfin da 'yan Sanda ke yi abu ne da ke sosai rai matuka tare kuma da nuna yadda mummunar dabi’ar ta nuna wariya ta samu gindin zama a Amurka''

Pelosi ta kara da cewa ''za’a cimma yin adalchi ne kadai wajen daukar kwararan matakai, kuma matakan da mu ke dauka ke nan ayau a matsayin matakin farko, a nan gaba akwai wasu masu zuwa nan da kwanaki kadan ta yadda Majalisa za ta gudanar da taron jin ba’asin jama’a dangane da dokar''

Shugabar majalisar wakilan ta Amurka ta ce ''Babu yadda zamu yi kasa a gwuiwa akai wajen samar da gagarumin sauyi abinda ya haifar da dokar shari’a da aikin 'yan Sanda wadda za ta cire shinge wajen hukunta 'yan Sandan da suka aikata laifi wajen la’akari da dokar su ta aiki da ke basu kariya''

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI