Coronavirus za ta haddasa kamfar abinci a duniya -MDD

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. REUTERS/Lisi Niesner

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadin cewar duniya na fuskantar barazanar karancin abinci wanda zai shafi miliyoyin jama’a saboda matsalar annobar coronavirus.

Talla

Guterres yace yanayin samar da abinci ya durkushe, yayin da annobar ta jefa mutane miliyanb 820 cikin yunwa, kuma miliyan 144 daga cikin su yara ne kanana masu kasa da shekaru 5, adadin dake nuna cewar cikin ko wadanne yara 5 a duniya daya daga cikin su na fuskantar wannan matsala.

Sakataren yayi gargadin cewar a cikin wannan shekara kawai za’a samu Karin mutane miliyan 49 da zasu afka cikin tsananin talauci, kuma muddin hukumomin da abin ya shafa suka kasa daukar mataki matsalar na iya fin yadda akayi hasashe.

Guterres ya bukaci daukar matakin kare ma’aikatan dake bangaren samar da abinci da masu aikin jinkai da kuma masu rarraba abincin a sassan duniya.

Sakataren ya kuma bukaci taimakawa yara kanana da basa zuwa makaranta da abincin da zasu ci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI