Coronavirus

Fiye da mutum miliyan 7 ke dauke da coronavirus a Duniya- WHO

Hukumar WHO ta bayyana yadda aka samu sabbin kamuwa da cutar fiye da dubu 130 cikin kasa da sa'o'i 24.
Hukumar WHO ta bayyana yadda aka samu sabbin kamuwa da cutar fiye da dubu 130 cikin kasa da sa'o'i 24. Wang Zhao / AFP

Fiye da mutum dubu dari 4 da uku hukumar lafiya ta duniya WHO ta tabbatar coronavirus ta kashe a sassan duniya, tun bayan bullarta cikin watan disamban bara a yankin Wuhan na tsakiyar China zuwa tsakar ranar yau Talata.

Talla

Cikin bayanan da WHO kan fitar kan halin da ake ciki game da cutar ta coronavirus a sassan duniya, ta bayyana yadda aka samu sabbin kamuwa dubu 131 da 296 wanda ke mayar da jumullar wadanda cutar ta kama zuwa mutum miliyan 7 da dubu 39 da 918.

Alkaluman na WHO sun kuma nuna cewa, yanzu haka jumullar mutum dubu 404 da 396 coronavirus ta kashe a sassan duniya inda Amurka ke da matattu dubu 110 da 915, kana Birtaniya da mutane dubu 40 da 542 sannan Brazil da mutum dubu 36 da 455 sai Italiya da mutane dubu 33 da 899 sannan Faransa da mamata dubu 29 da 155.

Nahiyar Amurka dai ce kan gaba a yawan masu dauke da cutar da mutum miliyan 3 da 366 da 251, kana nahiyar turai da mutum milyan 2 da 303 da 361 sannan gabashin Mediterranean da jumullar mutum dubu 658 da 614 kana kudancin Asiya da jumullar masu dauke da cutar dubu 378 da 118 tukuna yammacin Asiya da mutum dubu 192 da 335 sannan Nahiyar Afrika da jumullar masu dauke da cutar dubu 140 da 498.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI