Amurka

An gudanar da Jana'izar George Floyd a Houston

Akwatin da ke dauke da gawar George Floyd bakar fata dan Amurka da 'yansanda kasar suka kashe.
Akwatin da ke dauke da gawar George Floyd bakar fata dan Amurka da 'yansanda kasar suka kashe. REUTERS/Carlos Barria

Dubunnan jama’a suka raka gawar George Floyd zuwa makwancinsa na karshe bayan jana’izarsa a Majami’ar Houston da ke matsayin mahaifar bakar fatar dan Amurka da ‘yansandan kasar suka kashe, kisan da ya haddasa boren jama’a a sassa daban daban na duniya don nuna adawa da dabi’ar nuna wariya da kuma cin zarafin da ‘yansanda ke yiwa jama’a.

Talla

Gabanin jana’izar George Floyd da ta gudana a Houston, tun daga ranar Litinin an bayar da dama ga maziyarta masu fatan alkhairi fiye da dubu 6 shiga cikin majami’ar da gawarsa ta ke don yi masa bankwanan karshe.

Jana’izar ta Floyd mai shekaru 46 ta samu halartar fitattu daga ‘yan siyasan Amurka da masu fafutukar kare hakkin dan adam da kuma ‘yan kwallo, mawaka da ‘yan film ciki har da Channing Tatum da Jamie Foxx, baya ga dan damben boxing Floyd Mayweather.

Fadan majami’ar da ya jagoranci addo’in binne Floyd, Mia Wright ya ce za su yi kuka suyi mamako sannan suna da cikakken sa rai don tabbatar da adalci.

Tun farko guda cikin ‘yansanda Minneapolis ne ya dira gwiwarsa kan magogwaron George Floyd bayan kayar da shi kasa daure da ankwa a hannayensa biyu, yayinda sautin bidiyon kisan na Floyd da aka dauka, anji lokacin da ya ke fadawa dansandan cewa baya iya lumfashi, kalamin da ya zama abin da masu zanga-zangar adawa da nuna wariyar ke amfani da shi.

George Floyd aka binne shi Talatar nan a Houston gab da kabarin mahaifiyarsa, kisan na sa ya sake fito da barakar da ake da ita a Amurkan kan abin da ya shafi nuna wariya ga bakar fatar da ke can.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.