Halin da ake ciki dangane da coronavirus a duniya

Jami'an kungiyar Red Crox ke feshin magani coronavirus
Jami'an kungiyar Red Crox ke feshin magani coronavirus REUTERS/Ajeng Dinar Ulfiana

Ya zuwa ranar Laraba, Annobar Korona ta hallaka mutane dubu 411 da 588, cikin sama da mutane miliyan bakwai da suka kamu da cutar a kasashe 196 na duniya.

Talla

Mutane kimanin miliyan 7 da dubu 254, da 140, alkaluman hukumomin lafiyar kasa-da-kasa suka tabbatar na dauke da cutar koronavirus, kuma kimanin mutane miliyan 3 da dubu 214 da 600 suka warke.

Sai dai wadannan adadi ne kawai na wadanda gwaji ya tabbatar suna dauke da cutar, domin kuwa akasarin kasashen na gudanar da gwaji ne ga wadanda suka nuna alamu ko mu’amala da masu dauke da ita.

Har yanzu kasar Amurka cutar ta fi yiwa illa, inda da kashe mutane dubu 112 da 6 sai Burtaniya a matsayi na biyu da mutane dubu 40 da 883 da cutar da kashe, sai Brazil da ta rasa mutane dubu 38 da 406, Italiya kuwa mutane dubu 34 da 043 cutar ta kashe, sai kuma Faransa inda cutar ta aike da mutane dubu 29 da 296 barzau.

Kasar China, inda cutar da bulla a watan Disambar Bara, ta tabbatar da mutuwar mutane dubu 4 da 634 cikin mutane dubu 83 da 046 da suka kamu.

A jumlarce mutane dubu 185 da 130 cutar ta kashe a Turai cikin mutane miliyan 2 da 318 da 773 da suka kamu, Amurka da Canada sun rasa mutane dubu 119 da 958 cikin miliyan 2 da dubu 076 da 546 da suka kamu.

A Latin Amurka da Caribbean mutane dubu 69 da 372 cutar ta hallaka, a Asia coronavirus ta kashe mutane 20,581 sai Gabas ta Tsakiya inda cutar ta kashe mutane dubu 10, 887 sai kuma Nahiyar Afirka inda ta kashe mutane 5, 529 cikin dubu 203, 457 da suka kamu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI