McKennie ya caccaki Donald Trump kan nuna wariya

Shugan Amurka Donald Trump
Shugan Amurka Donald Trump REUTERS/Jonathan Ernst

Shaharerren dan wasan kwallon kafa na kasar Amurka Weston McKennie ya zargi shugaba Donald Trump da nuna wariyar launin fata, tare da caccakar shugaban kan hallayen da ya nuna bayan mutuwar bakar fatar nan George Floyd, da ya haddasa zanga-zangar a fadin duniya.

Talla

Dan wasan na tsakiya mai shekaru 21 ya bayyana haka ne yayin hira da mujallar wasanni Sport Bild ta kasar Jamus inda yake taka leda, yana mai cewa Trump bai cancanci zama shugaban kasa a matsayin sa na mai nuna wariyar launin fata kirikiri.

Floyd, wanda akayi jana’izar sa jiya Litinin, ya mutu ne lokacin da wani dan sanda farin fata ya durƙusar da guiwa a wuyansa a Minneapolis, na yankin Minnesota, a ƙarshen watan Mayu.

Mutuwar, wacce hoton bidiyo ya nuna, ta haifar da zanga-zanga a biranen Amurka da wasu sassan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.