Coronavirus

Adadin mutanen da coronavirus ta kashe ya kai dubu 416 da 343- WHO

Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus. Christopher Black/WHO

Zuwa tsakar ranar yau Alhamis fiye da mutum dubu 416 hukumomin lafiya suka tabbatar coronavirus ta kashe a sassan duniya dai dai lokacin da jumullar masu dauke da cutar ke tasamma miliyan 7 da rabi.

Talla

Alkaluman da hukumomin lafiya ke fitarwa game da cutar ta coronavirus kowacce rana, ya nuna cewa zuwa tsakar ranar yau litinin jumullar mutum dubu 416 da 343 cutar ta hallaka cikin adadin masu dauke da ita mutum miliyan 7 da dubu 383 da 140, da ke kasashe 196 tun bayan barkewarta karshen watan Disamban bara a yankin Wuhan na China.

Cikin bayanan WHO, ta bayyana yadda aka samu karin mutum dubu 105 da 621 sabbin kamuwa da cutar ta COVID-19 daga jiya zuwa yau a kasashen duniya 196, galibinsu a yankin kasashen Amurka.

Har yanzu dai Amurka ke sahun gaba a yawan mutanen da coronavirus ta kashe da jumullar mutum dubu 112 da 924 kana Birtaniya da dubu 41 da 128 tukuna Brazil da jumullar mamata dubu 39 da 680.

Sauran kasashen da coronavirus ta fi yiwa banna sun hadar da Italy da jumullar mamata dubu 34 da 114 kana Faransa da mamata dubu 29 da 319.

Hukumar lafiya ta duniya WHO dai ta bayyana cewa zuwa yanzu kusan mutum miliyan 2 da doriya suka warke daga cutar ta coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.