Jamus ta damu kan mamaye matsugunan Falasdinawa

Heiko Maas, ministan harkokin wajen Jamus
Heiko Maas, ministan harkokin wajen Jamus Michael Kappeler/Pool via REUTERS

Kasar Jamus da wasu kasashen Turai sun bayyana matukar damuwa dangane da shirin Isra'ila na kara mamaye wasu yankuna Falasdinawa a Gaban kogin Gaza.

Talla

Ministan Waje na Jamus Heiko Maas ya bayyana wannan damuwa yayin wata ziyara da ya kai birnin Kudus.

Ziyarar zuwa Isra'ila wadda itace ta farko da wani kusa daga kasashen Turai ya kai masu tun bayan fara fita daga annobar Coronavirus, Ministan wajen ya gabatarwa Hukumomin Israela sakon daga kasar Jamus da kuma wasu kasashen na Turai.

Ya fadi cewa suna fargaba matuka game da abinda zai faru bayan aiwatar da tsarin Isra'ilan na kara mamaye wasu yankunan.

Ita dai Isra'ila nan a shirin kara mamaye wuraren da take so ne , kamar yadda bukatar shugaban Amurka Donald Trump ke nunawa, inda suke ganin za su fara hakan ne daga ranar 1 ga watan gobe, wanda yazo daidai da ranar da Jamus za ta shugabancin Kungiyar Turai na karba-karba.

Ministan wajen ya fadawa taron manema labarai cewa yana ganin matakin Isra'ilan ya sabawa dokokin kasa da kasa, inda yake cewa abin bukata shine a koma tattaunawar sulhu don samun kasashe biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI