LeBron zai kafa kungiyar doke Trump a zaben Amurka
Wallafawa ranar:
Shahararren dan wasan kwallon Kwando LeBron James ya sanar da cewa shi da wasu fitattun ‘yan wasan motsa jiki, na shirin kafa wata kungiya mai karfi da zata kare ‘yan cin kuri’un Amurkawa bakaken fata, watanni biyar kachal kafin zaben shugaban kasar.
Wannan matakin ya kuma zo ne a yayin da zanga-zangar mutuwar bakar Fata George Floyte ta mamaye Amurka da wasu sassan duniya tare da kira da a kawo karshen daruruwan shekaru na nuna wariyar launin fata kan bakaken fata.
James yace, Kungiyar da zasu kira ta da “More Than A Vote”, zata rika wayar da kan Amurkawa ‘yan asalin Afirka yin rijistar zabe, da kuma karfafa musu guiwar fitowa kada kuri’unsu a zaben ranar 3 ga Nuwamba mai zuwa.
Kazalika, kungiyar za ta yaƙi da wariyar da ake nunawa Baƙaken fata a Amurka.
James, wanda ke da magoya baya fiye da miliyan 135 a shafukan sa na Twitter, Instagram da kuma Facebook, ya ce yana shirin yin amfani da kafofin sada zumunta wajen yakar duk wani yunƙurin taƙaita bada damar kada ƙuri'u ga kabilu mara rinjaye.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu