Sama da mutane dubu 5 annobar Korona ta kashe cikin sa'o'i 24

Ofishin wayar da kan jama'a na musamman saboda coronavirus a Mogadiscio na kasar Somalia
Ofishin wayar da kan jama'a na musamman saboda coronavirus a Mogadiscio na kasar Somalia REUTERS/Feisal Omar

Hukumar Lafiya at Duniya tace adadin mutanen da suka mutu sakamakon annobar COVID-19 ya kai 412,926, yayin da miliyan 3 da 227,700 suka warke a fadin duniya.

Talla

Alkaluman hukumar lafiyar sun ce mutane 5,015 suka mutu sakamakon cutar a ranar Laraba, yayin da aka samu sabbin masu dauke da cutar 125,128, yayin da Brazil ke sahun gaba wajen samun mutane 1,272 da suka mutu, sai Amurka mai sabbin mutane 1,027.

Har yanzu Amurka ke sahun gaba wajen mutuwar mutanen da cutar ta harba, inda take da 112,402, sai Birtaniya mai mutane 41,128, sannan Brazil mai mutane 38,406, sai italia mai mutane 34,114 sannan Faransa mai mutane 29,319.

Yanzu haka cutar ta kasha mutane 185,616 a Turai, 120,410 a Amurka da Canada, 69,604 a Kudancin Amurka, 20,639 a Asia, sai kuma 5,558 a Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI