Coronavirus

Adadin masu coronavirus ya zarta miliyan 7 da rabi a sassan duniya- WHO

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce adadin mutanen da annobar COVID-19 ta kashe a fadin duniya ya kai 421,691 yayin da cutar ta kama mutane sama da miliyan 7 da rabi, kana sama da miliyan 3 suka warke.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus. Fabrice COFFRINI / AFP
Talla

Alkaluman da hukumar ta bayar a yammacin yau Juma'a ta bayyana yadda annobar ta coronavirus ta kashe jumullar mutane dubu 113 da 820 a Amurka, kana wasu dubu 41 da 279 a Birtaniya sai kuma wasu dubu 40 da 919 a Brazil.

Alkaluman na WHO sun kuma bayyana yadda rayukan mutum dubu 34 da da 167 suka salwanta sanadiyyar cutar ta coronavirus a Italia kana wasu mutum dubu 29 da 346 wadanda cutar ta kashe a Faransa.

WHO ta ce a nahiyar Turai kadai coronavirus ta kashe mutane dubu 186 da 453 yayinda ta kashe wasu dubu 121 da 870 a kasashen Amurka da Canada yayinda ta kashe wasu mutane dubu 21 da 805 a nahiyar Asia tukuna wasu mutum dubu 5 da 904 a nahiyar Afirka, ko da dai hukumar ta ce akwai hasashen ninkuwar adadin wadanda cutar ta kashe a Afrikan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI