Babu laifi a salon shakar wuyan da 'yansanda ke yiwa mutane- Trump
Wallafawa ranar:
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce wani lokaci yana da muhimmanci 'yan Sanda su makure wuyar wanda ake zargi da aikata laifi duk da sukar matakin sakamakon kisan gillar da aka yiwa George Floyd wanda ya haifar da zanga zanga a ciki da wajen Amurka.
A wata hirar da yayi da tashar talabijin na Fox, Trump ya ce idan Dan Sanda ya na kokawa da wanda ake zargi da aikata laifi, shake wuyar sa ba laifi ba ne a wurin sa.
Trump yace zai baiwa hukumomin jihohi shawara kan cigaba da amfani da dabarar makure wuyar wadanda ake zargin idan bukatar hakan ta taso.
Shugaban yace yana bukatar Yan sandan su cigaba da gudanar da ayyukan su kamar yadda doka ta tanada da kuma nuna tausayi da jajircewa.
Kisan Floyd ya haifar da mummunar zanga zanga da kuma bukatar ganin an sake fasalin ayyukan Yan sandan da kuma daina amfani da makure wuyar wanda ake zargi da aikata laifi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu