Korona ta raba sama da mutane miliyan 44 da aikinsu a Amurka

Kasar Amurka ta sake samun mutane sama da miliyan guda da rabi da suka rasa gurabun ayyukan yi sakamakon annobar coronavirus, abinda ya kawo adadin wadanda suka rasa aiki a kasar zuwa sama da miliyan 44.

Yadda hada-hada ta katse a yankin Manhattan  a New York na kasar Amurka sakamakon killace jama'a
Yadda hada-hada ta katse a yankin Manhattan a New York na kasar Amurka sakamakon killace jama'a REUTERS/Mike Segar
Talla

Bayaga halaka dubban rayukan da take yi a Amurka, annobar coronavirus na cigaba da yin tasiri wajen janyowa tattalin arzikin kasar koma baya ta fuskoki da dama ciki harda tafka hasarar miliyoyin guraben ayyukan yi.

Ma’aikatar kwadagon kasar tace alkaluman mutanen da suka gabatar cewar sun rasa ayyukan su a makon jiya kuma suna bukatar tallafi ya kai miliyan guda da dubu 540.

Sakataren Baitulmalin kasar Steve Mnuchin yace ba zasu sake rufe harkokin kasuwanci ba a yunkurin su na ceto tattalin arzikin kasar daga rugujewa.

Rabon da a ga irin wannan matsalar ta rashin aikin yi a Amurka, tun bayan matsanancin matsin tattalin arziki a farkon karni na 20.

Yanzu haka kasar Amurka ke matsayi na farko wajen samun mutane sama da miliyan 2 da suka kamu da cutar, inda ta kashe 113,209.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI