Mutane kussan miliyan 4 suka warke daga coronavirus

Yadda ake gwajin cutar korona a Wuhan na kasar China
Yadda ake gwajin cutar korona a Wuhan na kasar China Hector RETAMAL / AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya tace adadin mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da annobar COVID-19 ya kai 417,773 a fadin duniya, yayin da cutar ta kama mutane kusan miliyan 7 da rabi.

Talla

Alkaluman da hukumar lafiya ta gabatar sun ce mutane miliyan 7 da dubu 417 da 773 suka kamu da cutar a fadin duniya, yayin da dubu 417 da 773 suka mutu, kana kuma miliyan 3 da dubu 308 da 400 sun warke.

Hukumar tace a cikin sa’oi 24 da suka gabata mutane 4,809 suka mutu, yayin da aka gano sabbin mutane 132,999 da suka harbu da cutar.

Kasar Amurka ke matsayi na farko wajen samun mutane sama da miliyan 2 da suka kamu da cutar, wadda ta kasha 113,209, sai Birtaniya wadda tayi asarar mutane 41,279, sannan Brazil a matsayi na 3 da tayi asarar mutane 39,680.

Nahiyar Turai kawai tayi asarar mutane 186,208, sai Amurka da Canada wadanda suka yi asarar mutane 121,254, sai Asia mai mutane 21,214 sannan Afirka mai mutane 5,676.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI