Saudiya ta fitar da fatawa kan dabi'ar kyamar Yahudawa

Wani Babban Malami a kasar Saudiya Mohammad al-Issa ya bada fatawar cewa  yaki da nuna kyamar yahudawa gagarumin aiki ne na addini.

Shugabannin kasashen larabawa lokacin taro kan rikicin Yeman
Shugabannin kasashen larabawa lokacin taro kan rikicin Yeman SPA / AFP
Talla

A wata tattaunawar fitaccen malamin Muhammad al-Issa da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP a Riyadh ya kafe da cewa lallai nunawa yahudawa kyama kuskure ne a koyarwar addini.

Malamin wanda tsohon Ministan shari'a ne ya ce Kungiyar Musulmi ta Duniya za ta ci gaba da gwagwarmayar yakar nuna kyamar yahudanci da wariyar launin fata.

Da asusun kudaden Saudiya ne dai ake tafiyar da kungiyar yakar masu adawa da yahudancin.

Malamin na kira ga mabiyan addinin Islama da Yahudancin da su dinke dukkan wata baraka.

Saboda matsayin Malamin, a watan Janairun da ya gabata sai da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yaba masa, a lokacin da Malamin ya yi tattaki zuwa Poland don halartan taron cika shekaru bukukuwan ‘yantar da sansanin mutuwa na ‘yan Nazi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI