shugaban 'Yan sandar Atlanta ya yi Murabus bayan kisan wani bakar fata
Shugaban yan sandan jihar Atlanta a kasar Amruka ya yi murabus, bayan wani dan sanda ya kashe wani matashi bakar fata mai shekaru 27 a duniya a kokarin kamashi da ya yi, al’amarin da ya haifar zanga zangogin da kone kone.Masu zanga zangar sun datse wata babbar hanyar mota, tare da kona wani gidan abincin ‘’fast food Wendy's’’ dake kusa da inda aka kashe Rayshard Brooks, sakamakon ja in ja da wani dan sanda, kamar yadda majiyoyin yada labaran yankin suka tabbatar.
Wallafawa ranar:
Magajin garin Atlanta, Keisha Lance Bottoms, dan demokrat da sunansa ya yi tambari a wajen a goyon bayan Joe Biden a zaben shugabancin Amruka da ake shirin yi a watan nowemba mai zuwa ne, ya bayyana murabus din 'Erika Shields, da ya share tsawon 20 ya na jagorantar rundunar yan sandan jihar Atlanta.
A dai bangaren kuma, a jiya assabar duban mutane ne suka gudanar da zanga zanga a Paris da kuma wasu biranen kasar Faransa, kamar yadda ta gudana a wasu biranen kasashen Suiss, Australia da kuma London, domin nuna rashin amincewarsu da nuna kabilanci da kuma cin zarafin da yan sanda ke yi wa jama’a
Zanga zangar da ta gudana a dandalin jamhuriya dake birnin paris ta yi nasarar hada kimanin mutane dubu 15 da suka halarce ta kamar yadda hukumomin kasar suka sanar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu