Coronavirus

Kusan mutum dubu 4 Coronavirus ta kashe a sa'o'i 24- WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce annobar coronavirus ta kashe mutane dubu 438 da 250 a fadin duniya, bayan ta kama mutane miliyan 8, da dubu 90,290, yayin da miliyan 3 da dubu 698,500 suka warke.

Wani asibitin da ke kula da masu coronavirus a jihar Californiar Amurka.
Wani asibitin da ke kula da masu coronavirus a jihar Californiar Amurka. REUTERS/Lucy Nicholson
Talla

A cikin sa’oi 24 da suka gabata, Hukumar ta WHO ta ce cutar ta kashe mutane dubu 3 da 851, yayin da aka samu sabbin kamuwa dubu 114 da 921.

Acewar hukumar akasarin wadanda cutar ta kashe sun fito ne daga kasashen Amurka mai yawan jama'a 671, sai Brazil mai mutane 627 sai kuma Mexico mai mutane 439.

Bayanan WHO ya nuna cewa a nahiyar Turai kadai cutar coronavirus ta kashe mutane dubu 188 da 834, sai Amurka da Canada da suka yi asarar mutane dubu 124 da 826, sannan yankin  Gabas ta Tsakiya da ke mutane dubu 12 da 234 da cutar ta kashe kana nahiyar Afirka mai mutane dubu 6 da 792.

Tun cikin watan Disamban bara ne cutar ta bulla karon farko a yankin Wuhan na tsakiyar China, sai dai bata bazu kasashen duniya ba, sai tsakiyar watan Fabarairu yayinda ta tsananta a watan Maris wanda ya tilastawa kasashe daukar matakan killace jama'a don dakile yaduwarta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI