Tsoffin shugabanin duniya sun daura damarar yaki da yanayi
An kaddamar da wata sabuwar kungiya da ta kunshi tsoffin shugabannin kasashen duniya da Ministocin Harkokin Waje da Jami’an Diflomasiya domin janyo hankulan gwamnatoci don ganin sun bada gudunmawarsu wajen kare muhalli da akalla kashi 30 nan da shekarar 2030.
Wallafawa ranar:
Kungiyar na karkashin jagorancin tsohon Sanatan Amurka kuma tsohon Jakada na Musamman a yankin manyan tafkunan Afrika, Russ Feingold.
Wata sanarwar hadin guiwa da mambobin kmungiyar suka fitar a yayin kaddamar da ita a ranar Laraba, ta bukaci shugabannin duniya da su zuba jari a muhalli a matsayin babban ginshiken farfado da tattalin arziki.
Kungiyar ta ce, bai kamata a yi sakaci da alfanun da za a samu daga wuraren da aka ba su kariya ba domin kuwa suna taka rawa wajen yaki da talauci da kare namun daji da yaki da dumamar yanayi, da kuma magance aukuwar annoba.
A halin yanzu dai, wannan sabuwar kungiya na burin gwamnatocin kasashen duniya da su bada gudunmawar kashi 30 kacal wajen kare muhalli nan da shekarar 2030, lura da cewa, masana kimiya sun yi kashedin cewa, karancin abin da ake bukata shi ne kashi 30 wajen kare halittun da ke rayuwa a doran kasa a yanzu.
Daya daga cikin mambobin kungiyar kuma tsohuwar shugabar Ireland Mary Robinson, ta ce, babu yadda za a cimma muradun yarjejeniyar dumamar yanayi ta birnin Paris har sai an kare halittu.
Sauran mambobin sun hada da tsohon Firaministan Habasha, Hailemariam Desalegn da Tzipi Livni, tsohuwar Ministar Harkokin Wajen Isra’ila da kuma Ernest Bai Koroma, tsohon shugaban Saliyo, sai Olusegun Obansajo, tsohon shugaban Najeriya da Ellen Johnson Sirleaf, tsohuwar shugabar kasar Liberia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu