Syria

Waiwaye kan yakin basasar Syria

Sama da mutane dubu 380 suka rasa rayukansu sakamakon yakin basasar Syria
Sama da mutane dubu 380 suka rasa rayukansu sakamakon yakin basasar Syria Abdulaziz KETAZ / AFP

Fiye da shekaru tara kenan da Syria ta tsunduma cikin yakin basasa, lamarin da ya haifar da miliyoyin ‘yan gudun hijirar da suka rasa muhallansu, yayin da mutane a kalla dubu 380 suka mutu a sanadiyar rikicin kasar.

Talla

A cikin watan Maris na shekarar 2011, zanga-zanga ta barke a Syria, inda al’ummar kasar suka bukaci sauyi a tsarin siyasar kasar bayan iyalan gidan Assad sun kwashe tsawon shekaru 40 suna mulki.

A cikin watan Yulin shekarar ce, wata kungiyar ‘yan tawaye masu dauke da makamai ta bulla a Syria, inda take samun tallafi daga kasashen Yammaci da kuma na Larabawa.

A shekarar 2012 ne, dakarun gwamnatin Assad suka kara kaimi wajen murkushe ‘yan tawaye, inda suka yi ta kaddamar da kazaman hare-haren jiragen sama musamman a tsakiyar birin Hama da ya kasance tungar masu adawa da shugaba Assad.

A ranar 21 ga watan Agusta na shekarar 2013, aka kai harin makami mai guba kan tungar ‘yan tawaye a kusa da birnin Damascus, al’amarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla dubu 1 400, amma gwamnatin Syria ta musanta hannu a wannan harin.

A shekarar 2014 kuwa, Kungiyar ISIS ta ayyana kafa daula a yankin da ta kwace a Syria da Iraqi.

A shekarar 2015, kasar Rasha wadda ta kasance babbar amniniyar Syria, ta fara kai hari don mara wa dakarun Assad baya.

A cikin watan Oktoban 2019 ne kuma, gwamnatin Turkiya ta kai hari kan mayakan Kudawa a Syria bayan ta ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda, yayin da a cikin watan Disamban barar, dakarun gwamnatin Syriar suka kai kazamin hari a arewacin Syria da zummar kwace tungar karshe daga hannun mayakan jihadi a Idlib.

A cikin watan Maris na bana na dai, aka cimma yarjejeniyar tsagaita musayar wuta karkashin jagorancin Rasha da Turkiya bayan kwashe watanni ana barin wuta a kasar ta Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI