Amurka da Najeriya sun gana kan zaben bankin Afrika

Ginin Bankin Raya Kasashen Afrika
Ginin Bankin Raya Kasashen Afrika Reuters

Kasashen Amurka da Najeriya sun tattauna kan rawar da Bankin Raya Afirka na AFDB ke takawa wajen bunkasa tattalin arzikin nahiyar da kuma matsalolin tsaron da suka adadbi Yankin.

Talla

A tattaunawar da suka yi ta waya, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo da takwaransa na Najeriya Geoffrey Onyeama sun bukaci bai wa bankin damar gudanar da tsaftacacen zabe ta hanyar dimokiradiya domin samun wanda zai shugabanci bankin a watan Agusta sakamakon barakar da aka samu a tsakaninsu.

Ministocin biyu sun tattauna rawar da bankin ke takawa da kuma yadda yake taimaka wa kasashen Afirka wajen bunkasa tattalin arzikinsu da samar da tsaro, inda suka jaddada matsayinsu na aiki tare wajen bai wa kowanne bangare damar zabin abin da yake so.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana matsayinta karara na goyan bayan sake takarar Akinwumi Adeshina, yayin da Amurka ke bayyana shakku duk da wanke shi daga zarge-zargen da aka yi masa.

A karshe Pompeo ya jajanta wa Najeriya kan kisan da Yan ta’adda da Yan bindiga suka yi a Najeriyar, da kuma batun bai wa Najeriya tallafin Dala miliyan 30 domin inganta bangaren kula da lafiyar ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI