Amurka

Trump ya nemi taimakon China kan zaben Amurka-Bolton

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na China, Xi Jinping
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na China, Xi Jinping 路透社

Tsohon Mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro John Bolton ya ce, shugaba Donald Trump ya roki shugaban China Xi Jinping da ya taimaka masa wajen samun nasara a zaben shugaban kasar da za a yi a wannan shekara.

Talla

Wani sashe na littafin da ya rubuta wanda fadar shugaban Amurka ba ta son ganin an gabatar da shi ga jama’a ya ce, samun nasarar zaben na tattare da shirinsa na  harkokin kasashen waje.

Wani yanki na littafin da Jaridun Washington Post da New York Times da Wall Street Journal suka wallafa ya ce, shugaba Trump a shirye yake ya kauda kansa daga yadda China ke cin zarafin Musulmi  'yan kabilar Uighur muddin ya taimake shi ya ci zabe.

Bolton ya ce, a lokacin da ya yi aiki da Trump, babu wani matakin da yake dauka da ba shi da nasaba da bukatar sake zabensa.

Tsohon Mai bada shawarar ya ce, a wani taro da Trump ya yi da shugaba Xi a watan Yunin bara, Trump ya mayar da shi wani dandalin neman goyan bayan China da rokon shugabanta wajen tabbatar da ganin ya samu nasara akai.

Bolton ya ce, a shirye yake ya wallafa kalaman da Trump ya yi wajen taron ba tare da sanya wata kalma da ba tashi ba, amma gwamnatin Republican ta ki amincewa da haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.