Trump yace zai hukunta wanda ya bada labarin boye shi

Shugaban Amurka Donald Trump ya kaddamar da bincike domin gano wanda ya tseguntawa manema labarai cewar an ruga da shi cikin wani dakin karkashin kasa lokacin da masu zanga zangar adawa da kisan da aka yiwa George Floyd suka kama hanyar zuwa fadar.

Shugaban Amurka Donald Trump yayin jawabi a fadar White House
Shugaban Amurka Donald Trump yayin jawabi a fadar White House Win McNamee/Getty Images/AFP
Talla

Jaridar New York Times ta ruwaito cewar jami’an tsaron dake kariya lafiyar shugaban sun dauke shi cikin gaggawa tare da matar sa Melania da dan su Barron inda aka ruga da su dakin dake karkashin kasa a fadar shugaban kasa ranar 29 ga watan Mayu domin kare lafiyar su.

Babban lauyan gwamnatin Amurka ya tabbatar da rugawa da shugaban ganin yadda al’amura suka tabarbare har ya kaiga masu zanga zangar sun fara tsallake shinge fadar White House, amma shugaba Trump yace ba haka abin yake ba.

Trump ya shaidawa jami’an sa cewar yana kokarin gano wanda ya tsegunta labarin domin hunkunta shi.

Kwana biyu bayan aukuwar lamarin, shugaba Trump yayi jawabi ga al’ummar Amurka inda yayi barazanar baza sojoji domin tinkarar masu zanga zangar, kafin daga bisani agan shi dauke da littafin Bible a hannun sa yana daukar hoto.

A ranar 3 ga watan Yuni shugaban yace alambaran babu wanda ya boye shi a fadar shugaban kasar, inda ya shaidawa tashar Fox News cewar babu gaskiya cikin labarin, amma Babban lauyan gwamnati William Barr yace ganin yadda lamarin ya tabarbare ya sa jami’an hukumar tsaron farin kaya dake kare lafiyar shugaban suka bukaci a ruga da shi karkashin kasa domin kare lafiyar shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI