WHO ta hana amfani da maganin Hydroxychloroquine kan masu korona

Kwayoyin maganin Hydroxychloroquine, da a baya ake amfani da shi wajen warkar da zazzabin malaria.
Kwayoyin maganin Hydroxychloroquine, da a baya ake amfani da shi wajen warkar da zazzabin malaria. AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO / OMS ta bayyana dakatar da amafani da maganin Hydroxychloriquine wajen warkar da masu dauke da cutar coronavirus a asibitoci, sakamkon rashin tasirinsa wajen rage kisan da cutar ke yi.

Talla

A ranar Laraba WHO ta bayyana dakatar nazarin da kwararru ke yi kan Hydroxy-chloriquine wajen gwajinsa a matsayin maganin cutar ta korana a karo na biyu, kana Jumma'an nan kuma ta sanar da matakin daina amfani da ita a asibitoci kan masu dauke da coronavirus.

WHO ta ce, ta dauki wannan matakin ne, sakamakon gwaje-gwajen da kwararrunta sukayi ya nuna cewa Hydroxychloroquine, da ake dade ana amfani da shi wajen warkar da zazzabin cizon saura, baida tasari wajen rage yawan mace-mace da coronavirus ke haddasawa.

Tana mai cewa, akai wasu gwaje-gwajen da akeyi kan wasu magun-gunan na daban, wadanda ake ganin tasirinsu fiye da wannan, don haka bai kamata arika bata lokaci wajen amfani da abin da baida tasiri ba.

To sai Hukumar Lafaiyar ta Duniya ta bakin shugaban sashin kimiyyarta Soumya Swami-nathan, har yanzu ana ci gaba da binciki don gano ko hydroxychloroquine zai iya zama rigakafin covid -19 ko a’a.

Manyan kasashe da wasu shugabanni ciki harda shugaban Amurka Donald Trump sun amince da maganin Hydroxychloroquine amatsayin waraka ga cutar korona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.