MDD

MDD ta bukaci yin bincike kan cin zarafin bakake a Amurka

Wasu masu zanga-zangar kyamar nuna wariya a Amurka.
Wasu masu zanga-zangar kyamar nuna wariya a Amurka. REUTERS/Jim Bourg

Hukumar Kare Hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gudanar da bincike kan tsarin da ake bi wajen cin zarafin bakaken fata ‘yan assalin Afirka da ke rayuwa a Amurka bayan ta yi Allah- wadai da matakin.

Talla

Hukumar mai wakilai daga kasashe 47 na duniya ta amince ba tare da hamayya ba  da kudirin da kasashen Afirka suka gabatar wanda ya bai wa shugabar hukumar Michelle Bachelet damar gudanar da binciken da kuma gabatar da rahoto a cikin shekara guda.

Taron Hukumar ya yayyafa ruwa kan bukatar kasashen Afirka na kafa kwamitin bincike na musamman da zai gudanar da bincike a Amurka, inda ya bukaci hukumar ta gudanar da binciken da kanta.

Kasar Amurka ta fice daga cikin wannan hukuma shekaru biyu da suka gabata saboda abin da ta kira sukar matakan wariyar da Israila ke nunawa Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.