Najeriya

Najeriya ta yi watsi da zargin da Birtaniya ta yi mata kan Kirista

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Solacebase

Najeriya ta yi watsi da wani rahotan bincike da Majalisar Dokokin Birtaniya ta yi wanda ya zargi kasar da musguna wa mabiya addinin Kirista da kuma yadda ake kashe su a cikin kasar.

Talla

A sanarwar da mai taimaka wa shugaban kasa wajen harkokin yada labarai Garba Shehu ya sanya wa hannu, Najeriya ta ce tana iya bakin kokarinta wajen ganin ta samar da yanayi mai kyau da kuma tsaron da ya dace ta yadda kowanne dan kasa zai gudanar da addininsa a inda yake bukata ba tare da tsangwama ba.

Sanarwar ta ce, kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare kan Kiristoci da mujami’u da zummar raba kan jama’a, duk da yake tana kai irin wannan harin kan Musulmi da Masallatai, amma shugaban kasa wanda Musulmi ne da mataimakinsa wanda Kirista ne sun jajirce wajen daukar matakan shawo kan matsalar.

Shehu ya ce ,Najeryia za ta ci gaba da sauke nauyin da ke kanta wajen hada kai da kawayenta domin murkushe mayakan Boko Haram domin tabbatar da tsaro a yankin arewacin kasar, tare da lalubo hanyar sasantawa da kuma kubutar da duk wadanda kungiyar ta yi garkuwa da su, ba tare da la’akari da addininsu ba.

Gwamnati ta ce, tana iya bakin kokarinta wajen ganin ta hada kan al’ummar kasar ta hanyar tattaunawa wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ke jagoranci, yayin da gwamnatin tarayya da na jihohi ke daukar matakan sasanta rikicin da ake samu tsakanin manoma da makiyaya, wanda za ta gabatarwa jama’a cikin makwanni masu zuwa.

Shehu ya kuma ce gwamnatin ta tashi tsaye wajen shawo kan labaran karya da ake yadawa ta kafofin sada zumunta wadanda ke matukar illa a cikin kasar.

A karshe sanarwar ta ce, gwamnati za ta ci gaba da aiki da duk bangarorin da suka damu da halin da ake ciki a Najeriya da kuma kasashen waje domin magance duk matsaloli da ake da su wajen tabbatar da ‘yancin bil'adama da bai wa jama’a damar gudanar da ayyukansu da addininsu ba tare da tsangwama ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI