Lafiya

Za samar da allurar rigakafin Coronavirus nan da karshen 2021

Wani asibiti da ake kulawa da masu Coronavirus
Wani asibiti da ake kulawa da masu Coronavirus REUTERS/Lucy Nicholson

Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana fatan cewa, za a samar da daruruwan miliyoyin alluran riga-kafi annobar COVID -19 kafin karshen wannan shekarar, wanda tace zai iya kaiwa biliyan 2 a shekarar 2021.

Talla

Yayinda aka shiga rige-rige ko gasa wajen samar da maganin rigakafin na Coronaviorus, Daraktan Kimiyya na WHO Soumya Swami-nathan ta ce, yanzu haka akwai kimanin magungunan daban-daban har 200 a fadin duniya da ake gwaje-gwajensu a asibitoci, wanda tace, za’a iya dacewa da daya ko biyu kafin karshen wannan shekara.

Babbar jami'ar hukumar ta WHO ta bayyana rukunin mutane uku cikin al’umma da tace, za’a fara baiwa maganin da zaran an same shi, da suka hada da jami’an kiwon lafiya da na ‘yan sanda da kuma gajiyayyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI