Amurka

Kotu na shirin sallamar Kassim Tajideen a Amurka

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a kungiyar Hezbollah
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a kungiyar Hezbollah REUTERS/Mohamed Azakir

Kotu a Amurika na shirin sallamar wani hamshakin dan kasar Lebanon da ake tuhuma da kasancewa daya daga cikin masu tallafawa kungiyar Hezbollah,sallamar dake zuwa shekaru biyu kafi kawo karshen hukuncin dauri da aka yanke masa na zama kurkuku,gani cewa ya na fama da rashin lafiya.

Talla

Ranar 28 ga watan Mayu ne wata kotu a Washington ta amince da bukatar sallamar Kassim Tajideen mai shekaru 64 da ake kyautata zaton ba shida isasar lafiya ganin ta yada wutar Coronavirus ke yaduwa da kuma rashin lafiya da yake fama da ita, ana sa ran Kassim Tajideen ya koma kasar sa ,a dai dai lokacin da sallamar sa ke ci gaba da haifar da cece kutse.

Sai dai lauyan na sa ya bayyana cewa ana kokarin shafawa Kassim kashin kaji a wannan lokaci da ya dace kotu ta sallame shi daga wannan tuhuma da ake masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI