Coronavirus

Adadin wadanda COVID-19 ta kashe ya kai dubu 464 da 423 a sassan Duniya

Wasu masu dauke da COVID-19 a Brazil
Wasu masu dauke da COVID-19 a Brazil AFP / MICHAEL DANTAS

Akalla mutum dubu 464 da 423 cutar covid-19 ta hallaka a sassan duniya tun bayan bullarta a China karshen watan disamban bara, ind ake da mutum fiye da miliyan 8 da suka kamu da cutar ko da dai akwai mutane fiye da miliyan 3 da suka warke.

Talla

Alkaluman da kamfanin dillancin labaran Faransa ya fitar a yau Lahadi ya nuna cewa har aynzu Amurka ke da yawan masu dauke da cutar haka zalika mamata da mutum dubu 119 da 719 kana Brazil da mamata dubu 49 da 976 sai Birtaniya da mutane dubu 42 da 589 wadanda coronavirus ta kashe.

Can a Iran karo na 3 kenan a jere adadin mutanen da Coronavirus ke kashewa cikin kasa da sa’o’I 24 na zarce 100, matakin da ya mayar da adadin mutanen da cutar ta kashe zuwa dubu 9 da 623.

Tun cikin watan Fabarairun da ya gabata ne Iran ta samu bullar cutar, inda a yanzu ta ke matsayin kasar da tafi asarar rayukan al’umma tsakankanin takwarorinta kasashen gabas ta tsakiya.

Yanzu haka dai Iran na da jumullar mutum dubu 204 da 952 masu dauke da cutar bayan samun sabbin kamuwa dubu 2 da 368.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.