Saudiya-Hajji

Takaitattun mutane za a sahalewa gudanar da hajjin bana- Saudiya

Hukumomin Kasar Saudi Arabia sun sanar da cewar za su gudanar da aikin Hajjin bana amma ga takaitattun mutanen da suka fito daga kasashen duniya sakamakon annobar coronavirus.

Miliyoyin Mahajjata bara a kasa mai tsarki.
Miliyoyin Mahajjata bara a kasa mai tsarki. REUTERS/Waleed Ali
Talla

Ma’aikatar kula da aikin Hajjin kasar ta ce sabanin yadda aka saba mutane kadan ne za su gudanar da ibadar, wadanda suka kunshi jami’ai daga kasashen duniya amma ba tare da maniyatan da suka saba zuwa sauke farali ba.

Kafin dai wannan lokaci kasashen duniya da dama na ta ko kwanton yadda za’a gudanar da aikin Hajjin bana saboda illar da annobar COVID-19 ta yiwa kasashen duniya, ciki harda kasar ta Saudi Arabia.

Tuni wasu kasashen Musulmai suka sanar da cewar ba zasu halarci ibadar ta bana ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI